BANGAREN DABI'U

Amsa: Annabi - tsira da aminci su tabbata a gare shi - ya ce: "Mafi cikar muminai imani mafi kyawunsu a ɗabi'u". Tirmizi da Ahmad ne suka ruwaito shi.

Amsa: 1. Domin cewa su sababi ne na soyayyar Allah - maɗaukakin sarki -.
2. Kuma sababi ne na soyayyar halitta.
3. Kuma su ne mafi girma a ma'auni.
4. Kuma ana ninka lada da sakamako saboda kyawawan ɗabi'u.
5.Kuma alama ce ta cikar imani.

Amsa: Daga Al-ƙur'ani mai girma, Allah - maɗaukakin sarki - Ya ce: {Lallai wannan Al-ƙur'anin yana shiryarwa ga (halaye) waɗanda suke mafi daidaita}. [Surat Al-Isra'i: 9]. Daga Sunna ta Annabi kuma: inda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - ya ce: "Kaɗai ni an aiko ni ne don in cika kyawawan ɗabi'u". Ahmad ne ya ruwaito shi.

Amsa: Kyautatawa: Shi ne jin tsoron Allah a koda yaushe, da kuma shinfiɗa alheri da kyautatawa ga halittu.
Annabi - tsira da Amincin Allah su tabbata agareshi - ya ce: "Lallai Allah ya wajabta kyautatawa akan kowanne abu". Muslim ne ya ruwaito shi.
Daga cikin nau'ukan kyautatawa :

- Kyatatawa acikin bautar Allah - maɗaukakin sarki - ta hanyar tsarkake niyya acikin bautar sa.
- Kyautatawa ga mahaifa, ta hanyar faɗa da kuma aikatawa.
- kyautatawa ga zumunci da 'yan uwa.
- Kyautatawa ga maƙoci.
- Kyautatawa ga marayu da miskinai.
- Kyautatawa ga wanda ya munana maka.
- Kyautatawa a zance.
- Kyautatawa a tattaunawa.
- Kyautatawa ga dabbobi.

Amsa: Kishiyar kyautatawa ita ce munanawa.
* Yana daga haka:
Barin tsarkake niyya acikin bautar Allah - maɗaukakin sarki -.
* Da saɓawa iyaye.
* Da yanke zumunci.
* Da mummunar maƙwabtaka.
* Da barin kyautatawa zuwa ga talakawa da miskinai da wanin wannan, na abinda ya shafi munanan maganganu da kuma ayyuka.

Amsa:
1. Amana acikin kiyaye haƙƙoƙin Allah - maɗaukakin sarki -.
Surorinsu:
Amana acikin yin ibadu na abinda ya shafi Sallah, da Zakkah, da Azimi, da Hajji, da kuma waninsu, na daga abinda Allah Ya wajabta akan mu.
2.Amana a cikin kiyaye haƙƙoƙin halittu:
- Daga abinda ya shafi kiyaye mutuncin mutane.
- Da dukiyoyin su.
- Da jinanan su.
- Da sirrikan su, da dukkan abinda mutane suka amintar da kai akan sa.
Allah - maɗaukakin sarki - Ya faɗa acikin ambatan siffofin masu rabauta. {Sune waɗannan da suke ga amãnõninsu da alƙawarinsu mãsu tsarẽwa ne}. [Surat: Al-Mu'uminun: 8].

Amsa: Ha'inci, shi ne tozarta haƙƙoƙin Allah - maɗaukain sarki -da kuma haƙƙoƙin mutane.
Annabi - tsira da aminci su tabbata agareshi - ya ce: "Alamomin munafiki uku ne"- A ciki sai ya ambaci: "Idan aka amince masa sai ya yi ha'inci". Anhaɗu akansa (Bukhari da Muslim suka rawaito shi).

Amsa: Shi ne bayar da labari da abinda yake ya yi daidai da yadda abin yake, ko kuma abin akan yanda yake.
Daga surorinsa:

Gaskiya acikin zance da mutane.
Gaskiya acikin alƙawari.
Gaskiya akowacce magana da kuma kowanne aiki.
Annabi - tsira da aminci su tabbata agareshi - ya ce: "Lallai gaskiya tana shiryarwa zuwa ga aikin alheri, kuma lallai aikin alheri yana shiryarwa zuwa ga Aljanna, kuma lallai mutum zai yi gaskiya har ya kasance cikakken mai gaskiya". Anhaɗu akansa (Bukhari da Muslim suka rawaito shi).

Amsa: Karya. Ita ce kuma saɓanin haƙiƙa, daga wannan: Yi wa mutane ƙarya, da saɓawa alƙawaruka, da shaidar ƙarya (zur).
Annabi - tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai ƙarya tana shiryarwa zuwa fajirci, kuma lallai fajirci yana shiryarwa zuwa wuta, lallai mutum zai dinga yin ƙarya har sai an rubuta shi cikakken maƙaryaci a wurin Allah". Anhaɗu akansa (Bukhari da Muslim suka rawaito shi). Annabi - tsira da aminci su tabbata agareshi - ya ce: ("Alamomin munafiki uku ne" sai ya ambata daga ciki: "Idan ya bada labari sai ya yi ƙarya, kuma idan ya yi alƙawari ya saɓa". Anhaɗu akansa (Bukhari da Muslim suka rawaito shi).

Amsa: Haƙuri akan bautar Allah - maɗaukakin sarki -.
- Haƙuri akan ƙin yin saɓo.
- Haƙuri akan abubuwan da Allah ya ƙaddara masu raɗaɗi, da kuma godewa Allah akowanne hali.
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Allah Yana son masu haƙuri 146}. [Surat Aal Imran: 146]. Annabi - tsira da aminci su tabbata agareshi - ya ce: ’’Mamaki ga lamarin mumini, lallai al'amuran sa dukkannin su alheri ne, wannan bai zamo ga wani ɗaya ba sai mumini, idan farin ciki ya same shi sai yayi godiya, sai ya zama alheri gare shi, idan kuma cuta ta same shi sai ya yi haƙuri, shi ma sai ya zama alheri a gare shi". Muslim ne ya rawaito shi.

Amsa: Shine rashin yin haƙuri akan biyayya ga Allah, da kuma rashin yin haƙuri akan saɓawa Allah, da yin fushi akan abubuwan da Allah ya ƙaddara, ta hanyar maganganu da kuma ayyuka.
Daga cikin surorinsa:

$ Burin mutuwa.
$ Marin kundukuki.
$ Yaga tufafi.
$ Fizgar gasu.
$ Yi wa kai mummunar addu'a ta halaka.
Annabi - tsira da aminci su tabbata agareshi - ya ce: "Sakamako yana tare da girman bala'i, kuma lallai cewa Allah idan Ya so wasu mutane to sai ya Jarrabesu, wanda ya yarda (da Jarrabawar) to yardar tana gareshi, wanda kuma yayi fushi to fushin yana gareshi". Tirmizi da Ibn Majah ne suka ruwaito shi.

Amsa: Shi ne taimakon da mutane za su yi a taskanin su akan gaskiya da alheri.
Surorin taimakekeniya:

oTaimakekeniya acikin mayar da haƙƙoƙi.
o Taimakekeniya acikin juyar da azzalimi.
o Taimakekeniya acikin toshe buƙatun mutane da miskinai.
o Taimakekeniya akan kowanne alheri.
o Rashin taimakekeniya akan aikata laifi da cuta da shishshigi.
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Ku yi taimakekeniya akan aikin alheri da kuma tsoron Allah, kada kuyi taimakekeniya akan laifi da shishshigi, kuji tsoron Allah, lallai Allah mai tsananin uƙuba ne 2}. [Surat Al-Ma'idah: 2]. Annabi - tsira da aminci su tabbata agareshi - ya ce: "Mumini ga mumini tamkar gini ne, sashin sa yana ƙarfafar sashi". Anhaɗu akansa (Bukhari da Muslim suka rawaito shi). Annabi - tsira da aminci su tabbata agareshi - ya ce: "Musulmi ɗan uwan musulmi ne, kada ya zalunce shi, kuma kada ya miƙa shi, wanda ya kasance acikin buƙatar ɗan uwan sa Allah zai kasance acikin buƙatar sa, wanda ya yaye wani baƙin ciki daga musulmi Allah zai yaye wani baƙin ciki daga baƙƙan cikin ranar Al-ƙiyama daga gareshi, wanda ya suturta wani musulmi Allah zai suturta shi ranar Al-ƙiyama". Anhaɗu akansa (Bukhari da Muslim suka rawaito shi).

Amsa: 1. Jin kunyar Allah: Yana kasancewane ta hanyar kada ka saɓa masa - tsarki ya tabbatar masa -.
2. Jin kunyar mutane: Daga wannan akwai barin zance na alfasha mummuna da kuma yaye al'aura.
Manzon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata agareshi - ya ce: "Imani saba'in da wani abune" - ko: "Sittin da wani abune" - "Yanki, mafi ɗaukakar su: faɗin: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, mafi ƙasƙantar su; Gusar da ƙazanta daga hanya. Kunya wani yankine na imani". Muslim ne ya rawaito shi.

Amsa: - Tausayawa masu manyan shekaru, da kuma girmama su.
- Tausayawa masu ƙananan shekaru da kuma ƙananan yara.
- Tausayawa talaka da miskini da mabuƙaci.
- Tausayawa dabbobi shine ka ciyar da su, kuma kada a cutar da su.
Daga wannan faɗin Annabi - tsira da amici su tabbata agareshi -: "Kana ganin muminai a cikin jin ƙan su da soyayyr su kamar jiki ne, idan wata gaɓa ta koka, sai duka jikin ya ɗauka da rashin bacci da kuma zazzaɓi". Anhaɗu akansa (Bukhari da Muslim suka rawaito shi). Manzon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata agareshi - ya ce: "Masu jin ƙai Allah yana jin ƙan su, ku ji ƙan waɗanda ke bayan ƙasa sai wanda yake sama ya ji ƙan ku". Abu Daud da Al-Tirmizi ne suka ruwaito shi.

Amsa: Son Allah - maɗaukakin sarki -.
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma waɗanda suka yi imani sune mafi tsananin soyayya ga Allah}. [Surat Al-Baƙarah: 165].
Son Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -.
Ya ce:
"Na rantse da wanda raina yake a hannun Sa, ɗayan ku ba zaiyi imani ba har sai na kasance mafi soyuwa a gare shi daga mahaifin sa da kuma ɗan sa". Bukhari ne ya rawaito shi.
Son Muminai, da kuma son alheri gare su kamar yadda kake so wa kanka.
Annabi - tsira da aminci su tabbata agareshi - ya ce: "Dayanku ba zaiyi imani ba har sai ya sowa ɗan uwansa abin da yake sowa kan sa". Bukhari ne ya rawaito shi.

Amsa: Ita ce sakin fuska, tare da farin ciki da murmushi da tausasawa, da bayyanar da farin ciki a lokcin haɗuwa da mutane.
Ita ce kuma kishiyar ɗaure fuska a fuskar mutane daga abinda zai kore su.
Acikin falalaR hakan hadisai da yawa sun zo, daga Abu Zarr - Allah ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce da ni: "Kada ku wulaƙanta wani abu daga aikin alheri, koda kuwa ka haɗu da ɗan'uwan ka ne da sakakkiyar fuska". Muslim ne ya rawaito shi. Manzon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata agareshi - ya ce: "Murmushin ka a fuskar ɗan'uwan ka sadaka ne". Al-TirmiZi ne ya ruwaito shi.

Amsa: Ita ce fatan gushewar ni'ima daga wani, ko kuma ƙyamar ni'ima ga wani.
Allah - maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma daga sharrin mai hassada idan ya yi hassada 5}. [Suratu Falaƙ: 5].
Daga Anas ɗan Malik - Allah ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kada ku ƙi juna, kada ku yiwa juna hassada, kada ku juyawa juna baya, ku kasance - yaku bayin Allah - 'yan'uwan juna. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Amsa: Shine izgili ga ɗan'uwan ka musulmi, da wulaƙantar da shi, wannan baya halatta.
Allah - maɗaukakin sarki - Ya ce dangane da hani daga hakan: {Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada waɗansu mutãne su yi izgili game da waɗansu mutãne, mai yiwuwa ne (abin yi wa izgilin) su kasance mafifita daga gare su (mãsu izgilin), kuma waɗansu mãtã kada su yi izgili game da waɗansu mãtã mai yiwuwa ne su kasance mafĩfĩta daga gare su. Kuma kada ku aibata kanku, kuma kada ku jẽfi jũna da miyãgun sunãye na laƙabõbĩ. Tir da sũna na fãsiƙanci a bãyãn ĩmãni. Kuma wanda bai tũba ba, to, waɗannan sũ ne azzãlumai 11}. [Suratul Hujurat: 11].

Amsa: Shi ne kada mutum ya ga kan sa (mafifici) akan mutane, kada ya wulaƙanta mutane, kada kuma yaƙi gaskiya.
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma bayin Mai rahama su ne waɗanda suke tafiya a bayan ƙasa cikin sauƙi}. [Suratul Furƙan: 62]. Wato: Masu ƙanƙar da kai. Manzon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kuma wani ɗaya bazai ƙankar da kai ga Allah ba face sai Allah ya ɗaukaka shi". Muslim ne ya ruwaito shi. Manzon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai Allah ya yi wahayi zuwa gareni cewa ku ƙanƙar da kanku, ta yadda babu wani ɗaya da zai yi alfahari a kan wani ɗaya, kuma kada wani ɗaya ya yi zalinci akan wani ɗaya". Muslim ne ya ruwaito shi.

Amsa: 1. Girman kai akan gaskiya, shi ne ƙin karɓar gaskiya da rashin karɓar ta.
2. Girman kai ga mutane, shi ne, shi ne wulaƙantar da su, da maida su ba ba'abakin komai ba.
Manzon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata agareshi - ya ce: "Ba zai shiga Aljanna ba wanda duk ya kasance akwai kwatankwacin ƙwayar zarra na girman kai acikin zuciyar sa". Sai wani mutum ya ce: Lallle mutum yana son tufafin sa ya kasance mai kyau, takalmin sa ya kasance mai kyau? Sai ya ce: "Lallai Allah mai kyau ne, kuma yana son kyau. Girman kai shi ne ƙin gaskiya da wulakanta mutane". Muslim ne ya rawaito shi.
- Kin gaskiya: Dawo da ita.
- Wulaƙanta mutane: Wulaƙanta su.
- Tufafi mai kyau, da takalmi mai kyau basa cikin girman kai.

Amsa: - Algus a siye da siyarwa, shi ne ɓoye aibin dake jikin haja (Abin siyarwa).
- Algusu a neman ilimi, misalin wannan algusun da ɗalibai suke yi acikin jarabawa.
- Algus a magana, kamar shaidar ƙarya (shaidar zur).
- Kin cika alƙawari da abinda kake faɗa, da kuma abinda kake ittifaƙi dashi tare da mutane.
Acikin hani daga algus, lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya wuce wani shuri na abinci, sai ya sanya hannun sa acikin sa, sai 'yan yatsun sa suka samu danshi, sai ya ce: " Menene wannan ya kai mai wannan abincin? Sai ya ce: Ai ruwan sama ne ya zuba acikin su ya Ma'aikin Allah, sai ya ce: "Shin ba ka sanya shi a saman abin cin ba, domin mutane su gan shi? Duk wanda ya yimana algus to baya tare da ni". Muslim ne ya rawaito shi.
Subrah:
Shi ne shuri na abinci.

Amsa: Itace ambaton ɗan'uwanka musulmi da abinda ba yake ƙi, alhali ba ya nan.
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma kada sashinku ya yi gulmar sashi, shin ɗayan ku zai so ya ci naman ɗan'uwan sa a mace, to kun ƙi shi, ku ji tsoron Allah, lallai Allah Mai yawan karɓar tuba ne kuma Mai jin ƙai ne 12}. [Suratul Hujurat: 12].

Amsa: Shi ne ɗaukar zantuttuka tsakanin mutane, domin ɓatawa tsakanin su.
Manzon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata agareshi - ya ce: "Mai annamimanci ba zai shiga Aljanna ba". Muslim ne ya rawaito shi.

Amsa: Ita ce jin nauyin aikata alheri, da duk abinda aikata shi ya wajaba akan mutum.
Yana daga wannan:
Kasala acikin aikata wajibai.
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Lalle ne munãfukai sunã yaudarar Allah, alhãli kuwa Shi ne mai yaudarasu; kuma idan sun tãshi zuwa ga sallah, sai su tãshi sunã mãsu kasãla, suna nũnawa mutãne, kuma ba su ambatar Allah sai kaɗan}. [Surat Al-Nisa'i: 142].
To yana kamata ga mumini ya bar kasala da sanyin jiki da son zama, (yayi ƙoƙari) a tafiya acikin aiki da kazar-kazar da ƙoƙari da dagewa a wannan rayuwa da abinda zai yardar da Allah - Maɗaukakin sarki -.

Amsa: 1. Fushi abin yabo: Shi ne kuwa ya kasance domin Allah, idan kafIrai ko munafukai ko wasun su suka keta alfarmar Allah - tsarki ya tabbatar masa -.
2. Fushi abin zargi: Shi ne fushin da zai sanya mutum ya aikata ko ya faɗi abinda baya kamata.
Maganin fushi abin zargi.
Yin alwala.
Zama, idan ya kasance a tsaye yake, da kuma kwanciya idan ya kasance a zaune yake.
Ya lazimci wasiyyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - acikin wannan: "Kada ka yi fushi".
Ya riƙe ran sa daga afkawa wani abu ayayin fushin.
Neman tsarin Allah daga Shaiɗan abin jefewa.
Yin shiru.

Amsa: Shi ne leƙe da bincikar al'aurorin mutane da abinda suke ɓoye shi (ba sa so a gani).
Daga cikin surorin sa waɗanda aka haramta:

- Tsinkaya akan al'aurorin mutane acikin gidaje.
- Neman jin mutum zuwa zancen wasu mutane ba tare da sanin su ba.
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kada ku yi binciken ƙwaƙwaf...}. [Suratul Hujurat: 12].

Amsa: Barna ita ce kashe dukiya ba tare da haƙƙinta ba.
Kishiyarsa:
Rowa: Ita ce kamewa daga haƙƙinta.
Abinda yake daidai shi ne kasantuwa tsaka-tsakiya tsakaninsu, kuma musulmi ya kasance mai karamci ne.
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma waɗanda suke idan sun ciyar, bã su yin ɓarna, kuma bã su yin ƙwauro, kuma (ciyarwarsu) sai ta kasance a tsakãnin wancan da tsakaitãwa}. [Suratul Furƙan: 67].

Tsoro: Shi ne ya ji tsoron abinda bai kamata ya ji tsoronsa ba.
Misalin jin tsoro daga faɗin gaskiya, da kuma hana mummunan abu.
Gwarzantaka:
Ita ce gabatowa akan gaskiya, wannan kamar gabatowa a fagagen fama domin kare Musulunci da musulmai.
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - ya kasance yana faɗa acikin a addu'ar sa: "Ya Ubangiji ina neman tsarin Ka daga tsoro". Manzon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: “Karfaffan mumini ya fi alheri da soyuwa a wurin Allah daga Mumini rarrauna, a kowanne akwai Alheri”. Muslim ne ya rawaito shi.

Amsa: Misalin tsinuwa da zagi.
- Da kuma misalin faɗin wane: "dabba", ko ire-irensu daga lafuzza.
- ko ambaton al'aurori daga kalmomin alfasha da muni.
- Haƙiƙa Annabi - tsirada amincin Allah su tabbata agareshi - yayi hani daga wannan gaba ɗayansa, sai ya ce: "Mumini ba mai yawan sukar mutane bane, kuma ba mai yawan tsinuwa bane, ba kuma mai batsa bane, haka ba ya mummunar magana". Al-Tirmizi da Ibn Hibban ne suka ruwaito shi.

Amsa: 1. Addu'a akan Allah ya azurta ka da kyawawan ɗabi'u, ya kuma taimaka maka akan haka.
2.Jin tsoron Allah - mai girma da ɗaukaka -, da cewa shi Yana sane da kai, Yana kuma jin ka, Yana ganin ka.
3. Tuna ladan kyawawan ɗabi'u, da kuma cewa su sababi ne na shiga Aljanna.
4. Tuna mummunar makoma ta munanan ɗabi'u, kuma cewa su sababi ne na shiga wuta.
5. Kuma su kyawawan ɗabi'u suna janyo soyayyar Allah da soyayyar halittar sa. Kuma su munanan ɗabi'u suna janyo fushin Allah da kuma fushin halittar Sa.
6. Karanta tarihin Annabi - tsira da aminci su tabbata a gare shi - da kuma koyi da shi.
7. Abota da mutanan kirki, da kuma nisantar mutanan banza.